Join/Login and make your voice heard Connect With Other Naijatipsland Members

CISLAC ta yi Allah wadai da halin yunwa da fatara da yayi sanadiyyar mutuwar mutane a turmutsitsi


Daraktan cibiyar CISLAC Kwamared Auwal Musa Rafsanjani, ya yi Allah wadai da matsanancin yunwa da tsananin talauci da ya addabi ‘yan Najeriya, yana mai zargin gazawar gwamnati wajen magance matsalolin tattalin arziki da ke kara jefa al’umma cikin wahala.

Da yake tsokaci kan turmutsitsin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama yayin rabon kayan tallafi a sassa daban-daban na kasar, Rafsanjani ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici wanda ya nuna irin mawuyacin hali da al’ummar Najeriya ke ciki.

“Wannan yana nuna cewa ‘yan Najeriya suna fama da mawuyacin hali a karkashin wannan gwamnati,” in ji shi. “Abin takaici, gwamnati ta gaza daukar matakan da suka dace don magance matsalar da ita kanta ta kara tabarbarawa.”

DAILY POST ta rawaito a Abuja, turereniya yayin rabon kayan abinci a Cocin Katolika ta Holy Trinity da ke Maitama ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 10, ciki har da yara hudu, tare da jikkata wasu da dama. Shaidu sun bayyana cewa cunkoson fiye da mutum dubu daya ya haifar da lamarin a safiyar Asabar.

Haka zalika, a Okija, Jihar Anambra, rabon shinkafa da wani hamshakin dan kasuwa, Cif Ernest Obiejesi, ya shirya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 tare da jikkata wasu fiye da 30. Rahotanni sun bayyana cewa cunkoson jama’a ya haddasa turereniyar kafin a fara rabon kayan.

A Ibadan, Jihar Oyo, wata liyafar yara da kungiyar Women in Need of Governance and Support (WINGS) ta shirya karkashin jagorancin Sarauniya Naomi Silekunola, ta rikide bayan cunkoson jama’a ya haddasa turereniya. Yara da dama sun rasa rayukansu, yayin da wasu suka jikkata yayin kokarin shiga wurin taron.

Rafsanjani ya bayyana wadannan lamuran a matsayin abin da za a iya kaucewa idan gwamnati ta yi aiki tuƙuru don magance matsalolin talauci da yunwa.

“Dole ne gwamnati ta dauki matakai cikin gaggawa don magance rashin abinci, samar da ayyukan yi, da rage wahalhalun jama’a,” in ji shi.

Ya kuma jaddada cewa matsalar tsaro a kasar na taimakawa wajen tabarbarewar lamarin, inda ya ce rashin tsaro ya hana manoma yin noma, wanda ke rage samar da abinci. Ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta mayar da hankali kan samar da tsaro da bunkasa bangaren noma, tare da jan hankalin gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi su kara kokarin karfafa harkokin noma don rage zaman kashe wando da hijirar kauye zuwa birni.





Source link

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

0 Comments
Newest
Oldest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments
0
Would love your thoughts, please comment.x
()
x
Nigeria's Fast-Growing Online Forum
Logo
Verified by MonsterInsights
situs togel sydneylotto situs toto toto slot https://sih3.kepriprov.go.id/berita/ https://fast.indihome.web.id/slot/ https://uninus.ac.id/ togel online terpercaya bento4d situs toto situs toto bento4d